Abubuwan da za ki tanada:
Gurjajiyan kwakwa, Ruwan tafasasshen kanunfari, Garin dabino, Garin soyayyan ridi, nono, zuma:
Yadda za ki hada:
Za ki samu wadannan kayan hadin sai ki hade su wuri daya ki gauraya ki markada ki tace ki zuba nono da Zuma ki juya ki dunga sha.
Karin Bayanai
Za ki samu kankana ki markada a blender ki saka garin ridi a ciki da madara da zuma ku sha ku biyu.
Maganin sanyi
Hulba na mutukar kashe kwayoyin cuta da hana zubar ruwa, shan sa a ruwan zafi da zuma, ko diban garin a hadiye da ruwa ko yoghurt yana mutukar kashe kwayoyin cuta. Haka a jika da ruwa na minti ko a dafa a riga tsarki ko zama da shi sau biyu a rana yana kashe cututtukan sanyi.