Dakin ibadar aljannar duniya wato “temple of heaven”, wuri ne inda sarakunan zamanin daulolin Ming da Qing suke yin addu’a ga sama da hatsi, kuma yana gabashin kofar Zhengyang. Siffar sashen wurin da ke arewa kewayayyiya ce, siffar sashen da ke kudu kuwa mai dungu 4 ne, wannan ya alamta cewa, siffar dakin ta sama a kewaye take, amma a kasa, tana da dungu 4 ne. Dakin abadar aljannar duniya na birnin Beijing na da bangwaye biyu, sun kuma raba dakin kashi biyu, daga ciki da waje, fadinsa ya kai hekta 273, yawancin gine-gine suna cikin sashe na ciki na dakin ibadar.
An gina dakin ibadar aljannar duniya na birnin Beijing ne a shekarar 1420 wato shekara ta 18 ta zamanin Yongle na daular Ming, daga baya aka sake gyara shi a zamanin Jiajing na daular Ming da zamanin Qianlong na daular Qing, hakan ya sa dakin ya kara girma da kuma kwarjini. Ana iya cewa, dakin wata alama ce ta tsohuwar wayewar kan gabashin kasashen duniya bisa tsoffin al’adu da tsarin manyan gine-gine da yake da su.
Dakin ibadar aljannar duniya na Beijing yana nuna mana fasahar gine-gine mai inganci ta zamanin daulolin Ming da Qing, gaskiya wuri ne da jama’a za su kashe kwarkwatan ido sosai, kana ya kasance gine-ginen da ake muhimman addu’o’i na zamanin da na kasar Sin. An tsara gine-gine masu inganci, kuma an kawata su yadda ya kamata, yana kuma da muhimmin matsayi a tarihin gine-ginen kasar Sin, kana wata dukiya ce mai daraja ta fasahar gine-gine ta duniya.
Tarihin dakin ibadar aljannar duniya
An fara gina dakin ne a shekarar 1420, sarkin Chengzu Zhu Di na daular Ming ya kwashe shekaru 14 yana jagorancin aikin gina dakin wurin ibadar aljannar duniyar tare da fadar sarakuna. A wancan lokaci, an sanya wa wurin suna dakin ibadar sama da kasa. Ya zuwa shekarar 1530 ta daular Ming, aka gudanar da bikin yin addu’a ga sama da kasa a wurare biyu, kuma an mayar da dakin ibadar aljannar duniya a matsayin wurin yin addu’a ga sama, shi ya sa aka canja sunansa zuwa dakin ibadan sama wato dakin ibadar aljannar duniya a shekarar 1534. A shekarar 1747 ta daular Qing, sarkin Qianlong ya yanke shawarar cewa, zai sake gina bangwayen dakin ibadan, sakamakon haka, aka gyara wasu muhimman gine-gine a dakin ibadan kamar su babban dakin Qinian, da dakin adana ‘yan fallen tunawa da kaka da kakannin sarakuna, da dandalin Yuanqiu na yin addu’a ga sama da sauransu. Kawo yanzu, ba a gyara babban tsarin dakin ibadan ba. A halin da ake ciki yanzu, akwai bishiyoyi da yawa a kewayen dakin ibadar aljannar duniya kamar wani babban lambun shan iska da ke kudancin birnin Beijing.
Tsarin gine-ginen dakin ibadar aljannar duniya.
Akwai bangwaye guda biyu da suka kewaye dakin ibadar aljannar duniya na birnin Beijing, muhimman gine-ginen suna cikin bangaren gidan dakin. Akwai wani dogon bango da ya ratsa dakin kashi biyu wato daga kudu zuwa arewa. Bangaren arewa shi ne dandalin yin addu’a ga hatsi, inda ake yin addu’a a yanayin bazara domin kara girbin hatsi mai albarka, babban ginin dake tsakiyar dakin da ke cikin gidan daga arewa shi ne dakin Qinian.
Dandalin Yuanqiu yana sashin kudancin dakin, a kan gudanar da bikin yin addu’a ga sama a rana ta farko ta yanayin sanyi, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, ginin dake tsakiyar dakin, shi ne babban dandalin dutse mai suna Yuanqiu. Akwai wata gada mai suna Danbi, ba ta da tsayi sosai wadda ta hada dandalolin biyu wato na Qinian da Yuanqiu, nisan da ke tsakaninsu ya kai mita 360. Daga kudu zuwa arewa, gaba daya tsawon hanyar da ke tsakiyar dakin ibadar ya kai mita 1200, a gufena biyu na hanyar kuwa, an dasa bishiyoyi masu yawa.
An gina dakin azumi a bangaren kudu na kofar Xitian, wuri ne inda sarakuna suke yin azumi kafin su yi addu’a. A yammacin dakin ibadar, an kafa hukumar kide-kide domin kula da shirin atisayen kide-kiden yin addu’a. Muhimman gine-ginen da ke cikin dakin ibadar, sun hada da dakin Qinian, da dakin Huangqian, da dandalin Yuanqiu, da dakin adana ‘yan fallen tunawa da kaka da kakannin sarakuna, da dakin yin azumi da dakin da aka gina da duwatsu kawai, ban da wannan kuma, akwai sauran wurare masu ni’ima kamar su bango mai amsa amo, da duwatsu uku masu amsa amo, da duwatsu bakwai masu alamar taurari bakwai da sauransu.
Muhimman wurare masu ni’ima na dakin ibadar aljannar duniya:
Dakin Qinian
Dakin Qinian yana arewacin dakin ibadar aljannar duniya, a da, ana kiran dakin da suna dakin Daqi ko dakin Daxiang, an gina shi ne a shekarar 1420 a zamanin daular Ming, shi ne gini mafi dogon tarihi na dakin ibadar aljannar duniya.
Kowace shekara, sarakuna su kan gudanar da bukukuwan yin addu’a ga sama a dakin Qinian domin neman samun yanayi mai kyau da girbin hatsi mai albarka, an kewaye dakin Qinian da launin shudi, saboda launin sama shudi ne, shi ya sa aka kawata dakin da launin shudi domin alamta sama.
Yayin da masu ziyarar bude ido suka shiga dakin Qinian, idan suka hangi kudu sosai, to, za su ga wata doguwar hanyar da ta yi kudu, har ta kankance kamar ta fado daga sama. Kan wannan, wani masanin gine-gine ‘dan kasar Faransa wanda ya taba ziyartar dakin ibadar aljannar duniya ya ce, ko da yake ginin zamani ya fi dakin Qinian tsayi, amma bai fi shi girma ba, kuma bai sa jama’a tunani mai zurfi kamar yadda dakin Qinian ke yi ba, domin bai kai matsayin fasahar dakin Qinian ba.
Bango mai amsa amo
Bangon da ke amsa amo yana kewayen dakin Huangqiongyu, gaban bangon yana da santsi, shi ya sa, yake amsa amon sauti. Idan mutane biyu suka tsaya a gefuna biyu na bangon a nisan mita dari daya ko biyu tsananinsu, idan mutum guda ya yi magana kusa da bangon, dayan zai iya jin maganarsa, kana sautin murya za ta kara tsawo, wannan yana da ban sha’awa kamar wata cudanya ce tsakanin dan Adam da gumaka, shi ya sa ake kiransa da suna “bango mai amsa amo’’.
Dandalin Yuanqiu
A baya, ana kiran dandalin Yuanqiu da suna dandalin yin addu’a ga sama, ko dandalin yin addu’a, a kewayen dandalin, akwai wani dandalin dutse mai hawa uku, wuri ne da sarakuna suke yin addu’a ga sama a rana ta farko ta yanayin sanyi, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. An gina shi ne a shekarar 1530 a zamanin daular Ming, kuma an gyara shi a shekarar 1749 a zamanin daular Qing. Dandalin ya kunshi hawa na sama da tsakiya da kuma na kasa, yawan matakalan dutsen dandalin yana da nasaba da lamba tara, wadda ake dauka a matsayin lamba mai girma. A tsakiyar hawa na sama, akwai wani kewayen dutsen da ake kira da suna dutsen rana ko dutsen tsakiyar sama, idan ka tsaya kan shi, ka yi ihu ko ka buga shi, kana iya jin amon sautin.
Dakin ibadar aljannar duniya a idon Sinawa
Dakin ibadar aljannar duniya wuri ne da sarakuna suke yin addu’a ga sama, tunanin tsorata da nuna godiya da dakin ke nuna wa sama, ya samo asali daga sarakuna da ma daukacin jama’ar kasar Sin.
Kafin wannan, mun ambata a baya cewa, ana nuna girmamawa ga sama a dakin ibadar aljannar duniya ta hanyar amfani da fasahar gine-gine mai inganci, kuma an nuna kwarjinin sama ne ta hanyar yin amfani da lamba tara. Ban da wannan kuma, an nuna mafarkin Sinawa ta hanyar amfani da launi wato ana jin dadin zaman rayuwa a cikin halittu.
Muhimmin launin dakin shi ne shudi, wanda shi ne launi na sama. Sama kan samar da rayuwa ga bil Adam da sauran halittu masu rai. Launin marufin dakin Qinian da na Huangqiongyu da bangwayensu duk shudi ne. Dakin idabar aljannar duniya kamar wata duniya ce mai launin shudi. Hoton sararin sama mai launin shudi da ke bayan wannan dakin, yana alamta mafarkin da ke cikin zukatan Sinawa wato bil Adam na jin dadin zaman rayuwa tare a muhallin halittu mai inganci.
(Marubuciya: Jamila daga CMG Hausa)