Gwamnan Jihar Kano, Eng. Abba Kabir Yusuf ya nada mambobin sabon kwamitin gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars bayan da wa’adin wadanda ke jagorantar kungiyar ya kare.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.
- Ahmed Musa,Tangalashi, Yamalash Sun Samu Muƙami A Kano Pillars
- Zanga-zanga: Za Mu Yi Amfani Da Dandalin Eagle Square Ko Da Izini Ko Babu A Abuja
An zabo sabbin mambobin kwamitin gudanarwar ne duba da kwarewa tare da gogewarsu a fanni wasanni na kwallon kafa, inda za su yi aiki na wucin gadi na shekara guda, tare da yiwuwar sabunta kwantiragin su idan suka tabuka abin a zo a gani.
Sabbin Mambobin sun hada da wasu fitattu masu sharhi a harkar kwallon kafa da harshen Hausa, Abubakar Isah Dandago (Yamalash) a matsayin babban darakta a bangaren sadarwa ta zamani da kuma Ismail Abba (Tangalashi) a matsayin mataimaki.
Akwai kuma kaftin din tawagar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles), Ahmed Musa wanda ya samu matsayin babban jakadan kungiyar ta Kano Pillars inda ya taka leda a shekarun da suka gabata.
Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa, wadannan mutane za su yi amfani da dimbin ilimi da gogewar da suke da ita wajen tafiyar da harkokin kungiyar ta Kano Pillars FC.
Ana sa ran sabon kwamitin zai yi aiki kafada da kafada da ma’aikatar matasa da wasanni ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni domin bunkasa kungiyar Kano Pillars.