Tsohon shugaban Laberiya Samuel Doe ya jogoranci kasarsa karkashin mulkin soja da kuma na farar hula.
Samel Kanyon Doe an haife fe shi ranar shida ga watan Mayu na shekara 1951 a wani gari mai suna Tuzon dake Gabashin kasar Laberiya.
A wannan kauye ya fara makarantar Firamari har zuwa 1967 inda ya ci jarabawar shiga Sekandare.
Ya yi karatu a makarantar Sakadanri ta Zwedru amma tafiya ba ta yi nisa ba a ka kore shi daga wannan makaranta. Shekarunsa biyu rak a ciki. Daga nan ne sai aka dauke shi a aikin sojasoja.
Rahotani sun ce ya nuna kwazo matuka a cikin aikin soja.
A shekara 1975 ya samu matsayin Sajan.
Ya samu horo na musamman daga sojoji Amurika a shekara 1979. Kuma a wannan shekara ce ya kifar da mulkin shugaban kasa William Tolbert, ranar 12 ga watan Afrilu na shekara 1980, a yayin da kasar Laberiya ta fada cikin wani mummunan yanayi na tsadar rayuwa.
Da juyin mulkin ya yi nasara, sai ya nada kansa a matsayin Janar. Daga 1980 har zuwa 1985 ya shimfida mulkin soja na kama karya, amma duk fa haka a tsukin wannan shekaru biyar Liberiya ta kasance kasar Afirka da ta fi samun tallafi daga Amurika.
A shekara 1985 Samuel Doe ya fara shimfada demokradiya inda aka zabe shi shugaban kasa. To sai dai jam’iyun adawa sun ce an tafka magudi a wannan zabe inda daga nan ne kasar Laberiya ta sake fadawa cikin wani sabon rikicin siyasa.
Sau da dama an sha yunkurin kifar da shugaba Doe daga mukaminsa ba tare da cimma nasara ba. Sannu a hankali Amurika ta fara janye goyan bayanta daga Samuel Doe, inda aka samu bullar wasu kungiyoyin tawaye kamar na Independant Front da Prince Johnson ya jagoranta sai kuma NPLF na Charles Taylor.
Wannan kungiyoyi biyu sun hada kai domin kalubalantar Samuel Doe, sun yi nasarar cafke shi ranar tara ga watan Satumba na shekara 1990, inda su ka yi gudunwa-gunduwa da shi.
Wanda su ka kalli talabijin a daidai wannan lokaci, sun ga yadda ‘yan tawayen su ka yi ta jan gawarsa bisa titi suka yanke masa kunnuwa da sauran sassan jikkinsa abin babu kyan gani.