A shekarar 2025 a gundumar Qiemo dake jihar Xinjiang ta kasar Sin, wasu sabbin sassan dausayi da ake iya nomawa sun bayyana a cikin makeken yankin hamada. A ’yan shekarun nan, an gyara yankin rairayi zuwa gonaki, wadanda fadinsu ya zarce murabba’in kilomita 40 a gundumar Qiemo. A cikin sama da shekaru 10, an yi kokarin raya wasu sassan dausayi da ake iya nomawa a cikin yankin hamada dake jihar Xinjiang, inda fadin gonakin da ake noman hatsi ya karu zuwa murabba’in kilomita dubu 8 ko fiye, al’amarin da ya sa Xinjiang ta zama jihar da ta fi samun karuwar hatsi da ake nomawa a duk fadin kasar Sin. Wani babban manomi dake wurin, mai suna Liu Yong, ya ce “Mun cimma fata mai kima sama da zinari a wannan hamada”.
A bana ne ake cika shekaru 70 da kafa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai ta kasar Sin, inda ake yawan ganin irin wannan labari mai dadi a duk fadin jihar, kuma Xinjiang na kara janyo hankalin jama’a daga sassan kasa da kasa.
A shekara ta 2024, adadin baki ’yan kasashen waje da suka shiga jihar don yawon bude ido ya wuce miliyan 5, adadin da ya karu da kaso 46 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekara ta 2023. Wadannan baki ’yan kasashen waje sun zama masu gani da ido game da ci gaban jihar Xinjiang. Daya daga cikin sanannun mutane a shafukan sada zumunta na intanet, Ba’amurke Danny Haiphong, ya ce “A wasu lokuta, abubuwan da muke gani a kafafen yada labaran yammacin duniya, ba sa bayyana abubuwa masu kyau. Amma muna jin dadin rayuwa a jihar Xinjiang dake da yanayi mai annashuwa.”
A halin yanzu, akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali, da wadata da kyan muhalli a jihar Xinjiang, inda jama’a ke jin dadin rayuwa da aiki a wurin, al’amarin da ya shaida nasarorin muhimman manufofin da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ke aiwatarwa a jihar a sabon zamani. Kana, a karkashin wadannan manufofi, an samu manyan sauye-sauye, gami da dimbin nasarorin da ba a taba ganin irinsu ba a tarihin jihar, inda aka shiga wani muhimmin lokaci na samun babban ci gaba, da gagarumin sauyi, kana jama’a suna kara samun moriya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp