Assalamu Alaikum Dr., ina da tambaya kamar haka:
Mace ce ta shirya adashi wanda za a dinga zubi har tsawon shekara daya ko makamancin haka, sannan kudin da mutane ke ba ta na zubi tana sayan kaddarori da kayan ajiya ko sana’a irin su kaji, POS, sayar da kayan sanyi da makamantar haka da niyyar kada kudaden mutane su narke, cewa idan shekara ko lokaci ya zagayo za ta saida ta ba su abin da suka zuba. Shin hakan ya halatta alhali kayan nan da ta sayo zai yiwu ta yi riba ko ta fadi alhali masu kudin ba su da kaso ko hasara ciki? Allah Ya kara ma Dr. lafiya, basira da nisan kwana.
Wa alaikumus salam. Bai halatta ba, saboda ka’ida sananniya a Shari’a “Ba a sarrafa dukiyar wani sai da izninsa.”
Al’ada tana da tasiri a zamantakewa, ana komawa zuwa gare ta idan aka samu sabani wajan fahimtar HUKUNCI.
A Al’adar Bahaushe Adashi ajjiya ce kawai ba tare da sarrafawa ba, don haka bai halatta a yi kasuwanci da kudin amana ba sai da iznin mai shi.
Allah ne mafi sani.