Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ya kakabawa hukumar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu (SAFA) takunkumi saboda shigar da dan wasan da bai cancanta ba a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 tsakanin Afirka ta Kudu da Lesotho a ranar 21 ga watan Maris, 2025.
A cewar FIFA, matakin na SAFA ya saɓa doka ta 19 na kundin ladabtarwa na FIFA da kuma sashi na 14 na dokokin gasar cin kofin duniya ta FIFA da aka yi wa gyara a shekarar 2026, sakamakon haka, an mayar da nasarar zuwa ga kasar ta Lesotho inda aka canza sakamakon zuwa 3-0 a matsayin Lesotho ce tayi nasara.
- Kotu Ta Dakatar Da PENGASSAN, NNPCL Kan Katse Wa Matatar Ɗangote Ɗanyen Mai Da Iskar Gas
- Sin Da AU Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna A Fannin Hadin Gwiwar Raya Kimiyya Da Fasaha
Bugu da kari, an ci tarar hukumar SAFA har CHF 10,000, yayin da shi kansa Mokoena ya samu gargadin hukumar.
An sanar da wannan matakin ne a yau 29 ga watan Satumba, 2025 a karkashin dokokin FIFA, amma kuma har yanzu SAFA suna da kwanaki goma domin daukaka kara a gaban kwamitin daukaka kara na FIFA.
Tawagar Afirka Ta Kudu wadda Hugo Broos ke jagoranta a halin yanzu suna kan gaba a rukuninsu na C na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya, bayan da suka samu maki 17 daga wasanni takwas, amma kuma yanzu makin ya rikito zuwa 14 sakamakon zabtare maki 3 da hukumar FIFA ta yi musu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp