Tawagar ‘yan ƙwallon ƙafa ta matasa ‘yan kasa da shekara 20 ta Argentina ta lallasa ta Nijeriya da ci 4 a wasan zagaye na 16 na gasar cin Kofin Duniya da ake bugawa a ƙasar Chile.
Wasan ya gudana ne a filin Nacional Julio Martinez Pradonas da ke birnin Santiago a daren ranar Laraba, inda Argentina ta fara cin ƙwallaye biyu kafin a tafiya hutun rabin lokaci ta hannun Alejo Sarco da Maher Carrizo.
- Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
- Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Carrizo ya ƙara ƙwallo, yayin da Silvetti ya rufe wasan da ta huɗu, wanda ya bai wa Argentina damar zuwa matakin kusa da na ƙarshe.
Tawagar Nijeriya ta zo wannan mataki, bayan da ta doke Saudiyya da ci 3-2, ta kuma tashi canjaras da Colombia a wasannin da suka gabata.
A gefe guda kuma, Argentina ta doke Australia da Italiya kafin wannan nasara.