A ranar Talata ne wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Sagiru Rijiyar Zaki, ɗan shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe ƙanwarsa da kishiyar mahaifiyarsa.
Wanda aka yanke wa hukuncin, mazaunin kauyen Kutama ne da ke karamar hukumar Gwarzo, an same shi da laifin daɓa wa kishiyar mahaifiyarsa mai suna Rabi’atu Sagir wuka da kuma shaƙe ƙanwarsa Munawara da gyale wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsu duka.
- Nuna Sassauci Ba Mataki Ne Da Ya Dace Da Warware Yakin Harajin Kwastam Ba
- Illolin Da Manufar Haraji Kan Kayayyaki Ta Haifar A Kan Amerikawa
Da take jagorantar shari’ar, Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da hujjojinsu a fili ba tare da wata shakka ba.
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.”
A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2023, a unguwar Rijiyar Zaki da ke Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp