Babban Kotun Tarayya da ke Kano ta bai wa Gwamnatin Kano Umarnin bai wa, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, tarar Naira miliyan 10,000,000 saboda tauye masa hakkin da tauye masa ‘yanci da walwala.
Kazalika kotun ta ce Sarkin na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, yana da damar yin yawo a ko’ina a fadin Nijeriya.
- Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sauraren Shari’ar Masarautar Kano
- Sarki Biyu A Gari Ɗaya: Aminu Ado Ya Isa Kano
Kotun ta sake jaddada ikonta na sauraren shari’ar da Sarki Aminu Ado ya shigar gabanta.
Wannan hukuncin ya biyo bayan umarnin da Gwamnatin Jihar Kano ta bayar na jami’an tsaro su kama Sarkin ba tare da gamsasshen dalili ba.
A jiya Alhamis kotun ta zauna, inda ta dage zaman zuwa yau Juma’a gabanin yanke wannan hukuncin kan dambarwar Masarautar Kano tsakanin Sarkin Kano na 14/16, Malam Muhammadu Sanusi II da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.