Kotun koli ta masana’antu ta kasa ta dage shari’ar da gwamnatin tarayya ta kai kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) har zuwa ranar Juma’a.
A ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta bukaci kotun da ta umarci kungiyar ASUU da ta janye yajin aikin da ta shafe watanni bakwai tana gudanarwa.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu shine wakilin Gwamnati yayin da Shugaban ASUU ke wakiltar kungiyar acikin karar.
Al’amarin da ya zo gaban Mai shari’a Polycarp Hamman wanda Ministan Kwadago da Aiki, Sen. Chris Ngige, a madadin gwamnatin tarayya ya gabatar a madadin gwamnatin tarayya, yana rokon kotu da ta umurci ASUU da ta koma bakin aikinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp