Babbar kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Alkaliyar Alkalai, Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin wucin gadi na hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yunkurin gyarea Æ™aramar fadar Nasarawa.Â
Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da gwamnatin jihar, da babban lauyan gwamnati, da kuma masarautar Kano suka shigar, inda suka yi karar Sarki Aminu Ado shi kadai kan yunkurin gyara karamar fadar ba bisa Æ™a’ida ba.
Sarki Aminu Ado Bayero ya kasance yana amfani da fadar ne tun bayan komawarsa Kano, bayan da gwamnatin Kano ta rushe masarautun jihar da gwamnatin Ganduje ta kirƙiro.
Mai shari’a Dije Aboki ta bayyana a cikin hukuncin cewa, “An bayar da umarni na wucin gadi na hana wanda ake kara, ko wakilansa, ko masu zaman kansu, ko duk wanda ke alhaki wajen bin umarninsa daga rushewa da gyara da gina wani sashe na Gidan Sarki da ke Nassarawa.
Masu gabatar da kara sun gabatar da bukatarsu ne a ranar 9 ga watan Satumba, bisa goyon bayan wata takarda mai sakin layi 33 da Matawallen Kano, Alhaji Ibrahim Ahmed ya sanya wa hannu.