Kotu Ta Kama, Doyin Okupe, Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi Da Laifin Karkatar Da Kudade.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu, Doyin Okupe, Darakta-Janar na yakin neman zaben Shugaban Kasa na Peter Obi, da laifin karkatar da kudade.
- Peter Obi Na LP Ya Zaɓi Doyin Okupe Daga Ogun A Matsayin Mataimakinsa Na Wucin-gadi
- LP, Ta Kori Daraktan Yakin Neman Zaben Obi, Okupe Da Wasu 11 Kan Gaza Biyan Harajin Jam’iyyar
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da Okupe a shekarar 2019 a kan tuhume-tuhume 59 da suka hada da karkatar da kudade kimanin Naira miliyan 702.
An dai gurfanar da shi a gaban mai shari’a Ijeoma Ojukwu tare da kamfanoni biyu – Value Trust Investment Ltd da Abrahams Telecoms Ltd.
Akwai yuyuwar zuwa da karin bayanai kan wannan labarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp