Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Kano ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar, inda ta nemi dakatar da rabon kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano kason su.
Jam’iyar APC, ƙarƙashin shugabanta na jihar, Abdullahi Abbas, ta shigar da ƙarar tun cikin watan Nuwamba 2024, inda ta nemi a soke shugabancin shugabannin ƙananan hukumomi da NNPP ke riƙe da su, bisa hujjar cewa ba su ci zaɓe ta hanyar dimokuraɗiyya ba kamar yadda Sashe na 7(1) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya tanada.
Jam’iyyar ta kuma nemi kotu da ta hana Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Nijeriya (CBN), da Akanta Janar na Ƙasa raba kuɗaɗen zuwa ƙananan hukumomin na Kano.
Masu amsa ƙarar sun haɗa da:
Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC)
Hukumar Raba Kuɗaɗe da Tsare-Tsare (RMAFC)
Ministan Kuɗi
Mai binciken Kuɗ na ƙasa
Alƙalin-Alƙalai na Ƙasa
A hukuncin da Alƙali Simon Amobeda, ya yanke a ranar Litinin, ya ce ƙarar ba ta da tushe bare makama. Ya ce bayan kotun ɗaukaka ƙara ta yanke cewa babbar kotun jihar Kano ce kaɗai ke da ikon sauraron irin wannan ƙara, masu ƙara suka nemi janye ƙarar, amma ba su gabatar da takardar janye wa cikin kwanaki 14 da doka ta tanada ba.
Masu amsa ƙarar sun nemi a yi watsi da ƙarar da tara.
Lauyan Alƙalin-Alƙalai na Ƙasa ya buƙaci tarar miliyan 2.5
Lauyan Kano ya buƙaci naira biliyan 2
Lauyan KANSIEC ya buƙaci biyan naira miliyan 2, yana cewa sun sha wahala a shari’ar.
Lauyan shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 ya nemi miliyan 44
Alƙali Amobeda ya yanke cewa a yi watsi da ƙarar gaba ɗaya, ba wai a kore ta na ɗan lokaci ba, tare da ƙin bayar da tara ga masu amsa ƙarar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp