Kotun sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisun tarayya da na jiha a jihar Delta, a ranar Litinin ta kori Hon. Ngozi Omolie na jam’iyyar Labour (LP), a matsayin mambar Majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Aniocha/Oshimili a Majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Delta.
Baya nan, kotun ta dawo wa tsohon wanda ke kan kujerar, Hon. Ndudi Elumelu na jam’iyyar PDP kujerarsa a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben mamban Majalisar wakilai da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu a wannan mazabar.
- Jam’iyyar Labour Ta Yi Fatali Da Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Zababben Gwamnan Abia
- Dan Takarar Gwamnan Labour Party Ya Janyewa Binani Takararsa A Jihar Adamawa
Mr Okolie dai ya tumbuke tsohon shugaban marasa rinjaye Ndudi Elumelu ne a zabe ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da shi Elumelu ya kalubanci sakamakon a gaban kotu.
Okolie dai ya samu nasara ne da kuri’u 53, 879 da ya kayar da Elumelu mai kuri’u 33, 466.
Mr Elumelu, ya shigar da korafi ya na kalubalantar ingancin tsayar da Okolie a matsayin dan takara bisa zargin cewa bai cika sharuda da ka’idojin da dokokin zabe suka shimfida ba.
Ya ce, LP ba ta tsayar da Okolie ta hanyar da ya dace ba domin a cewarsa jam’iyyar ta gabatar da sunansa (Okolie) ne kawai a matsayin dan takara amma ba mambar jam’iyyar ba ne.
Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin A.Z. Mussa, wacce ke zamanta a garin Asaba, a hukuncinta ta amince Elumelu ne sahihin wanda ya ci zaben.
Don haka ne kotun ta zartar da hukuncin cewa Elumelu ne zababen dan majalisar mazabar.