Wata babbar kotun shari’ar addinin Musulunci da ke Kano ta bada umarnin sake rubuta wa shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu (Rarara) sabuwar takardar sammaci sabida kin mutunta gayyatarta.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rahoto cewa, Kotun, wacce ke zamanta a unguwar Rijiyar Zaki da ke birnin Kano wacce ke karkashin Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ce ta bayar da umarnin yayin zamanta na ranar Talata.
Ana karar Rarara ne kan kin biyan wasu kudaden wasu wayoyin salula da yake karba yana raba wa mutane daga hannun wani dan kasuwa mai suna Muhammad Ma’aji.
Yawan kudin dai ya kai kimanin Naira miliyan goma da dubu dari uku.
Lauyan mai kara Barista I. Imam ya shaida wa kotun cewa, wanda ake karar bai mutunta sammacin da aka kai masa ba saboda kin halartar zaman kotun.
Lauyan ya roki kotun da ta bayar da umarnin a kamo Rarara kasancewar ya raina kotun.
Sai dai ya kara da cewa bai san ko sammacin da aka ba wa wanda ake karar ya isa gare shi ba, ko kuma a’a.
Kotun ta tambayi jami’inta da ya kai sammacin, Isma’il Zuhudu, ko ya ba Rarara hannu da hannu, inda ya ce ya like masa takardar a kofar gidansa kamar yadda kotun ta yi umarni, sakamakon sun neme shi don ya bavshi hannu da hannu amma bai same shi ba.
Mai Shari’a, Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ya ce kasancewar wanda ake tuhuma bai zo ba kuma bai aiko ba, kotun ta yi masa uzuri saboda wannan ne karo na farko da ya yi haka.
Daga nan ne ya ba da umarnin a sake rubuta sabon sammaci ga Rarara a sake kai masa ko kuma like masa a kofar gidansa da ke kan titin gidan Zoo a Kano tare da wallafa sammacin a shafukan sada zumunta da kafafan yada labarai.
Kotun ta kuma sanya ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu, 2023 domin ci gaba da sauraran karar.