Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da karar da Sanata Mohammed Danjuma Goje, ya shigar a gabanta na kalubalantar korara da kwamitin jami’yyar APC na mazabar Kashere da ke jihar Gombe ya yi masa.
Kwamitin ya dakatar da Goje ne daga baya kuma ya kore shi daga APC a watan Afrilu, 2023.
- INEC Za Ta Gurfanar Da Wadanda Ake Zargi Da Aikata Laifukan Zabe
- Masarautar Zazzau Ta Dakatar Da Marafan Yamman Zazzau Kan Daukar Doka A Hannunsa
Kwamitin ya kore shi ne, bisa zargin kin shiga ayyukan gangamin yakin neman zaben APC a dukkan matakai har da na yakin neman zaben shugaban kasa da kuma yi wa ‘yan takarar majalisar dikokin jihar da tarayya zagon kasa a lokacin yankin neman zaben.
Goje ya kuma ki yi wa shugabannin jami’yyar da’a da kuma kin yin biyayya ga mahukuntan da ke jagorantar jam’iyyar a jihar.
An kori Goje daga APC ne, bayan da kwamitin APC na mazabar Kashere ya mika rahotonsa na binciken zargin da ake yi wa Goje.
A cikin rahoton kwamitin, ya gano cewa, zargin da ake yi wa Goje, ya tabbata, inda kwamitin ya bayar da shawarar a gaggauta dakatar da shi da kuma korarsa daga jam’iyyar.
Shugabancin APC na mazabar Kashere sun amince da rahoton kwamitin binciken, inda kuma babban kwamitin APC na jihar Gombe da sauran kwamitocin kananan hukumomi 11 na jihar, su ma suka amince da rahoton kwamitin da ya dakatar tare da korar Goje daga APC.
Bisa wannan dakatarwar ne da kuma korarsa, hakan ya sa Goje ya garzaya zuwa kotun don kalubalabatar matakin.
Sai dai, a hukuncin da alkalin babbar kotun da ke Abuja wadda mai shari’a alkali Obiora Egwatu ke jagoranta a zaman da ta yi a ranar Talata, ta yi fatali da karar da Goje ya shigar a gabanta na kalubalantar dakatar da shi da kuma korarsa daga APC.
Ko a ciki watan Mayu, kwamitin zartarwa na APC na kasa ya janye maganar korar Goje daga APC.
A cikin sanarwar da sakataren yada labarai na APC na kasa, Felix Morka ya fitar ya sanar da cewa, korar ta Goje an jingine ta a gefe har sai an yi nazari akan matakin da APC reshen jihar ya dauka.
Alkali Egwuatu ya tabbatar da cewa, korafin Goje na rashin yi masa adalci don ya kare kansa daga zarge-zargen da kwamitin ya yi masa, bai da wata hujja, domin kwamitin ya ba shi isashen lokaci don ya kare kansa.
Kotun ta ce Goje na sane da zarge-zargen da ake yi masa, musamman ganin cewa wata jarida ta wallafa zarge-zargen da ake yi masa, inda hakan ya ke da damar ya kare kansa da kuma ba shi damar lokaci da wurin da zai kare kansa.
A martanin da babban kwamitin APC na jihar Gombe ya yaba da hukuncin da kotun ta yanke.