Wata kotun majistare da ke Iyaganku aa Ibadan, a ranar Laraba ta tasa keyar wani mutum mai shekaru 46 Mutiu Balogun, gidan gyaran hali bisa zargin kashe wani dattijo mai shekaru 70 a duniya.
Balogun, wanda ba a bayyana adireshinsa ba, an tuhumi shi da laifin kisan kai, inda alkalin kotun Olasinmibo Sanusi-Zubair, ta ki amsar rokon wanda ake kara na neman hurumin hukunci.
- Gwamna Uba Sani Ya Kashe Fiye Da Biliyan 8 A Gina Makarantun Kimiyya A Kaduna
- Gwamnatin Tarayya Na Aiki Tuƙuru Don Haɓɓaka Masana’antun Magunguna – Gwamnati
Sanusi-Zubair ta umarci ‘yansanda da su mayar da fayil din karar ga daraktan kararrakin jama’a don neman shawarwarin shari’a, daga nan kuma ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 25 ga watan Yuni.
Dansanda mai shigar da kara Oladejo Balogun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Mayu, da misalin karfe 1.30 na rana a unguwar Mokola da ke Ibadan.
Balogun, ya ce wanda ake tuhumar ya yi sanadin mutuwar mutumin mai suna Yekini, ta hanyar dukansa a kirji wanda a cewarsa laifin ya ci karo da sashe na 319 na dokokin laifuka na Jihar Oyo na shekarar 2000.