A ranar Alhamis ne wata kotu da ke zamanta a yankin Kabusa, Abuja, ta yanke wa wani saurayi mai suna Kefas Usman, mai shekaru 31 hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari, bisa samunsa da laifin barazana ga tsohuwar budurwarsa sabida ta yi kokarin yanke alakar da ke tsakaninsu.
Alkalin kotun, Malam Abubakar Sadiq, ya yankewa Usman hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa tare da rokon kotun da ta yi masa sassauci.
Sai dai alkalin kotun ya ba shi zabin biyan tarar Naira N20,000.
Rundunar ‘yansandan ta gurfanar da Usman ne da laifuka uku da suka hada da cin zarafi, da barazana da kuma tsere wa daga hannun ‘yansandan.
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, S. O. Osho, ya shaida wa kotun cewa, wanda ake tuhumar ya yi barazanar cutar da tsohuwar budurwarsa, Eunice Samuel, bayan ta yanke shawarar yanke alakar da ke tsakaninsu.