Wata babbar kotun jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga wani Durodola Kayode Ogundele bisa laifin yiwa wata tsohuwa mai shekaru 85 fyade.
An gurfanar da Ogundele a gaban kotun da mai shari’a Monisola Abodunde ke jagoranta a kan tuhuma daya wacce itace fyade.
An bayyana cewa Durodola Kayode Ogundele, a ranar 15 ga watan Yuni, 2021 a Ayetoro Ekiti a karamar hukumar Ido/Osi ta jihar Ekiti, ya yi wa wata tsohuwa mai shekaru 85 fyade. Laifin ya ci karo da sashe na biyu na dokar hana cin zarafin Mata ta Jihar Ekiti, 2019.
Da take yanke hukuncin, Mai shari’a Monisola Abodunde ta ce, “Don haka ba ni da wata shakka cewa a karshe masu gabatar da kara sun tabbatar da hujjojin da suka dace, wadanda suke da kwakkwarar hujja a zahiri, cewa wanda ake karar da gangan ya yi wa tsohuwar fyade.
“An samu wanda ake tuhuma da laifin fyade wanda ya sabawa sashe na 2 na dokar ta’addanci ta jihar Ekiti ta 2019 kuma an yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai daidai da sashe na 2 (2) na jinsi na jihar Ekiti.