A yau Litinin kotun kolin Nijeriya ta jingine hukuncin karar da ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani ta shigar a kan sakamakon zaben gwamnan jihar da ya ayyana Gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara.
Alkalan kotun kolin biyar karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro sun jingine hukuncin bayan amsa bahasi daga dukkan bangarori biyun da abin ya shafa.
- Kotun Koli Za Ta Saurari Shari’ar Zaben Gwamnan Adamawa A Ranar Litinin
- Za Mu Garzaya Kotun Koli Don Daukaka Kara Kan Zaben Gwamnan Adamawa- APC
Lauyan Dahiru, Akin Olujimi ya roki kotun kolin da ta amince da ayyana zaben da Hudu Yunusa, Kwamishinan Zabe na INEC ya yi na kasancewarsa babban jami’in zabe kamar yadda sashe na 149 na dokar zabe ya yi.
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Fintiri.
Wasu Alkalai uku na kotun daukaka kara sun tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Adamawa ta yanke a ranar 28 ga Oktoba, 2023, inda ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris.
Aisha Dahiru, wadda aka fi sani da Binani, ‘yar takarar gwamna ta jam’iyyar APC a zaben, ta bukaci kotu da ta kori Gwamna Fintiri wanda dan jam’iyyar PDP, saboda rashin bin ka’idojin dokokin zaben 2022 na INEC.
A hukuncin da aka yanke, Alkalan uku na kotun daukaka kara a karkashin jagorancin Tunde Awotoye, ya ce Binani ta kasa tabbatar da zargin rashin bin dokar zabe a zaben gwamnan jihar Adamawa da aka yi a watan Maris.
Kotun ta ce, ta gaza tabbatar da ikirarin da ta yi na magudin zabe a rumfunan zabe 14,104 ba.