Kotun daukaka kara da ke zamanta a Jihar Kaduna, ta ayyana ranar Talata 22 ga watan Janairun 2025, domin yanke hukuncin karar da tsohon Wazirin Zazzau, Ibrahim Muhammad Aminu ya shigar gabanta, kan neman kotun ta tsige Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli daga karagar masarautar.
Aminu ya shigar da kara gaban kotun ne yana kalubalantar nadin Sarkin Zazzau, inda ya ce nadin an yi shi ne ba bisa ka’idojin zaben Sarkin Zazzau na 19.
Tsohon Wazirin Zazzau wanda a wancan lokacin, yana daga cikin masu zaben Sarkin Zazzau, ya shigar da kara gaban kotun yana tuhumar mutane 13 da laifi wajen rashin bin dokan nada Sarki Ambasada Nuhu Bamalli.
Daga cikin wadanda ya shigar da karar tasu, akwai Ahmad Nuhu Bamalli da Marigayi Limamin Kona, Malam Sani Aliyu da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad el-rufa da sauransu.
A yayin zaman kotun a shekarar 2023, lauya mai kare wadanda ake tuhuma, Barista Abdul Ibrahim, ya bayyana wa kotun cewa wanda ya kai karar bai da ikon jayayya da nadin sarki ko kuma neman tsige shi kan cewar ba shi a cikin wadanda suke da gadon sarautar, sannan kuma ba shi daga cikin wadanda suka tsaya takarar neman sarautar.
Tsohon Wazirin Zazzau ya shigar da karar ne ta hannun lauyansa, Barisata B M Bello, inda yake kalubalantar cancantar nadin Ahmad Nuhu Bamalli kan kujerar sarautar Zazzau.
Hakan, ya sanya kotun ta bayyana cewa ranar 22 ga watan Janairun za ta kawo karshen rikicin.
Â