Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta shawarci kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da gwamnatin tarayya da su yi sulhu ba ta hanyar kotu ba domin shawo kan rashin fahimtar da ke tsakaninsu.
Kotun ta shawarci bangarorin ne a jiya, yayin da take sauraron karar da kungiyar ASUU ta shigar kan hukuncin da kotun masana’antu ta kasa ta yanke a ranar 21 ga watan Satumba, inda ta umarci malaman jami’o’in da su dakatar da yajin aikin da suke yi. ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu.
Kotun daukaka kara ta ba bangarorin biyu wa’adin sa’o’i 24 da su sake tunani, su zauna su fito da wani kudiri da zai faranta wa ‘yan Nijeriya rai.
Mai shari’a Georgewill Biobele Abraham ne ya nemi bangarorin biyu a lokacin da suka gurfana a gaban kotun domin sauraren karar da kungiyar ASUU ta shigar kan hukuncin kotun masana’antu ta kasa.
Mai Shari’a Georgewill ya baiwa lauyan gwamnatin tarayya, Mista James Igwe SAN da na ASUU, Mista Femi Falana SAN, da su fara zama a matsayin lauyoyi, su dauki halin kishin kasa sannan su gabatar da matsayar su ga wadanda suke karewa.