Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar Litinin ta tabbatar da Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin Gwamnan Jihar Sakkwato.
A hukuncin da mai shari’a Mbaba Bassi ya yanke, ya bayyana cewa, babu wata illa a hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ta yanke na tabbatar da zaben gwamna Aliyu.
- Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Soke Zaben Kakakin Majalisar Kaduna
- ‘Yan Watanni Bayan Shigarsa Musulunci Ya Rubuta Al-Qur’ani Da Hannu A Garin Birnin Gwari
Kotun ta bayyana cewar, kotun sauraron kararrakin zabe ta yi daidai a hukuncin da ta yanke, wacce ta bayyana Aliyu da mataimakinsa Idris Gobir cewa, sun cancanci tsayawa takara kuma ba su gabatar da takardun bogi ba kamar yadda masu kara (PDP da dan takararta) ke ikirari ba.
Kotun ta bayyana cewa, masu karar sun kasa gabatar da hujjojin sabawa kundin dokar zabe a zaben Gwamnan Jihar Sakkwato da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.