Kotun daukaka kara ta tabbatar da gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa wanda kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta jihar ta sauke.
A cikin hukuncin da Kotun daukaka kara ta yanke, ta soke hukuncin da kotun ta yanke, wadda ta bayyana dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, David Ombugadu, a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukace Lauyoyin Su Mayar Da Kwafin Takardun Shari’ar
- Zargin Baɗala: Hisba Ta Kama Mata Da Maza A Zamfara
Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana Sule na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 307,209 a kan abokin takararsa Ombugadu wanda ya samu kuri’u 283,016.
Sai dai dan takarar PDP wanda bai gamsu da sanarwar da hukumar zaben ta yi ba inda ya kalubalanci sakamakon zaben a kotu.
A watan da ya gabata, kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ta yanke hukuncin soke zaben gwamna Sule tare da ayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai kuma Gwamna Sule ya daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke, wacce ta sauya hukuncin kotun da kuma tabbatar da zaben gwamna Abdullahi Sule.