Kotun daukaka kara da ke da zamanta a Abuja, ta yi watsi da bukatar dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar SDP a zaben 2023, Dakta Umar Ardo, da tabbatar da nasarar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.
A hukuncin na ranar Talata, kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren koke-koken zaben kujerar gwamna, wacce ta yi watsi da kalubalantar nasarar lashe zaben da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya yi.
- Zaben Nasarawa: ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaro Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka Kara
- An Saki Fursunoni 4,000 Don Rage Cunkoso A Gidajen Yari A Nijeriya
Haka kuma kotun ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren koke-koken zaben dan majalisar wakilan tarayya da ta jiha, da ta yanke hukuncin babu komai a zaben kujerar ‘yan majalisun jihar biyu.
Kotun daukaka karar ta rushe hukuncin kotun sauraren koke-koken zaben wacce ta rushe zaben dan majalisar jihar Honarabul Sunday Peter mai wakiltar karamar hukumar Guyuk da Honarabul Babangida Muhammad Njidda, da ke wakiltar mazabar Nasarawo-Binyeri a Karamar Hukumar Jada.