Kotun sauraron kararrakin zaben jihar Kano, ta yi watsi da karar da dan takarar Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdussalam Abdulkarim Zaura ya shigar.
Zaura na kalubalantar nasarar da dan takarar jam’iyyar NNPP, Rufa’i Sani Hanga ya samu, cewa, ba shi ne asalin dan takarar jam’iyyar NNPP ba Sanata Ibrahim Shekarau ne, tsohon gwamnan Kano, kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya.
Mai Shari’a I.P. Chima ya yi watsi da karar da cewa, bata cancanta ba kuma ya ci tarar mai shigar da karar da ya biya jam’iyyar NNPP da kuma Rufai Sani Hanga, dan takarar jam’iyyar kudi naira 600,000.