Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kaduna, ta bayyana zaben gwamnan jihar ya dan takarar jam’iyyar (APC), Sanata Uba Sani, nasara a matsayin gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammalu ba (Inconclusive).
Idan za ku tuna cewa LEADERSHIP ta rawaito cewa, jam’iyyar PDP da dan takararta, Rt. Hon. Isah Mohammed Ashiru, ya kalubalanci ayyana Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar Kaduna na ranar 18, ga watan Maris, 2023.
- Gwamnatin Kaduna Ta Nemi Saudiyya Ta Zuba Jari A Jiharta
- Kotu Ta Daure Wata Matashiya Kan Satar Katin Waya Na ₦275,400 A Kaduna
Ashiru ya bukaci kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben sabanin wanda INEC ta bayyana a baya.
Don haka kotun mai alkalai 3 karkashin jagorancin mai shari’a Victor Oviawe ya ba da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 24 da ke unguwanni bakwai na kananan hukumomi hudu.