Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Taraba da ke zamanta a Jalingo, ta kebe ranar da za ta yanke hukunci kan karar da dan takarar jam’iyyar NNPP, Farfesa Sani Yahya ya shigar, yana kalubalantar nasarar Gwamna Agbu Kefas, na PDP a zaben 2023.
Babban Lauyan jam’iyyar NNPP, Barista Ibrahim Isiyaku (SAN), ya nemi a sake duba sakamakon zaben inda ya nanata cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana sakamakon zaben ne bisa tsoro da tilastawa.
Kotun, ta kebe ranar da za ta yanke hukunci ne biyo bayan karbar takardun korafe-korafe da hujjoji daga bangarori biyun.
Barista Ibrahim Isiyaku (SAN), ya yi zargin cewa an samu rashin tantance masu kada kuri’a a lokacin zabe a wasu rumfunan zabe da aringizon kuri’u da sauya sakamakon zabe, da dai sauran kura-kurai.
Ya nanata cewa, bisa wadannan kura-kurai da aka samu lokacin zaben, ya ba su damar neman garzaya kotu domin soke sakamakon zaben.
Barista Isiyaku ya kara da cewa, tunda farko, hukumar zabe a jihar ta amince a cikin rahotannin da ta bayar cewa, aikin zaben ya fuskanci kalubalen tashe-tashen hankula sakamakon harbe-harben bindiga da sojoji da ‘yansanda suka yi.
Shima da yake zantawa da manema labarai, Lauyan Hukumar INEC, Barista Emeka Okoro, ya ce, sun shaida wa Kotun cewa, NNPP ba ta gabatar da wasu kwararan hujjoji da za su tabbatar da korafe-korafenta ba. Don haka, sun bukaci kotun da ta yi watsi da karar da jam’iyyar NNPP ta gabatar a gabanta.