Game da babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya kin tafarkin murdiya, wanda aka gudanar a ranar 3 ga wannan wata, mutane daga kasa da kasa masu halartar bikin sun ba da ra’ayoyinsu ciki har da kalmomin hadin kai, da yin kokari tare, da sauransu don nuna kyakkyawar fata ga makoma.
Bayan shekaru 80 da gama yakin duniya na biyu, an canja burin dan Adam. Zaman lafiya da samun bunkasa sun zama babban jigo na halin yanzu, kasa da kasa suna kokarin samun zamanantarwa. Amma a sa’i daya kuma, ra’ayin mai karfi ya cinye maras karfi ya sake bullowa, an kawo illa ga tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, wanda MDD ta zama cibiyarsa, da kuma kara fuskantar manyan kalubale a fannonin zaman lafiya, da bunkasa, da kiyaye tsaro, da sarrafa harkokin kasa da kasa. Bisa wannan yanayin tinkarar sabbin barazana da kalubale, yaya kasa da kasa za su yi?
Shugaba Xi Jinping ya ba da ra’ayin cewa, yana fatan kasa da kasa za su koya daga tarihi da kiyaye zaman lafiya don sa kaimi ga zamanantar da duk duniya baki daya, da samun makomar dan Adam mai kyau. Ra’ayin ya samu goyon baya daga kasa da kasa. Shugabar sabon bankin raya kasashen BRICS Dilma Rousseff ta bayyana cewa, jawabin shugaba Xi Jinping ya shaida ra’ayin bai daya na kasashen duniya masu goyon bayan samun bunkasa cikin lumana, da kuma fatan bai daya na sa kaimi ga zamanantar da duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp