Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD tayi Kira ga al’umma akan su ci gaba da kai rahoton cin zarafin da ake yiwa mata da kana nan yara a kafafen sada zumunta ta hanyar Manhajar nan ta GBV da cibiyar ta samar.
Jami’a mai kula da abubuwan da suka shafi jinsi ta cibiyar, Zainab Aminu ce ta bayyana haka a taron manema labarai da CITAD din take shiryawa kowanne wata.
Tace a watan Mayun da ya gabata an samu karuwar cin zarafi da Kusan Kashi 85 cikin dari idan aka kwatanta da watan Aprilu.
A cewar ta, wannan Karin da aka samu ya samo asali ne sakamakon wayar da kan mutane da cibiyar takeyi wajen kai rahoton da zarar abin ya faru Kuma an tabbatar da faruwar.
Zainab Aminu tayi Kira ga al’umma akan su dinga kai rahoto ga hukumomin gwamanti dama waɗanda bana gwamanti ba kamar, Hukumar kare hakkin Dan adam, da hukumar kare fararen hula da hukumar hana fataucin mata da kana nan yara ta NAPTIP da hukumar wayar da kan al’umma ta kasa da kuma hukumar Hisbah ta jihar Kano.
A karshe tace idan har mutane sukayi shiru basa kwatanta cin zarafin da akeyi musu tabbas za’a ci gaba da aikata wannan ta’asa.