Jimlar kudaden da ke yawo a hannun mutane ya ragu zuwa naira tiriliyan 5 a watan Maris na 2025, wanda ke nuna raguwa daga naira tiriliyan 5.04 da aka samu a watan Fabrairun 2025.
Wannan yana kara raguwa daga naira tiriliyan 5.24 a watan Janairun 2025, a cewar sabbin kididdigar kudi da bashi wanda Babban Bankin Nijwriya ya wallafa a shafinsa na intanet.
- Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)
- Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri
Naira da ke yawo a hannun mutane shi ne jimlar kudin da ke yawo a cikin tattalin arziki, wanda ke wakiltar kudin da ake samu don ma’amaloli na yau da kullun, saka hannun jari, da tanadi.
Raguwar kudin a hannun mutane na iya zama wani bangare na kokarin rage matsin lamba kan hauhawar farashin kayayyaki da samun daidaiton tattalin arziki.
Baya ga raguwar kudade a hannun mutane, ajiyar a bankin CBN ya karu zuwa naira biliyan 28.52 a watan Maris na 2025, daga naira biliyan 27.57 a watan Fabrairun 2025. A watan Janairun 2025, ajiyar ya kai naira biliyan 27.43.
A halin yanzu, ajiyar ko-ta kwana ba ta canza ba a naira miliyan 284.36 a cikin watanni uku.
Ajiyar banki yana nufin kudaden da Babban Bankin da bankunan kasuwanci ke rike da shi don tabbatar da hada-hadar kudade a cikin bangaren banki. Ci gaba da karuwar ajiyar bankuna wata alama ce ta kokarin CBN na tsare harkokin kudade da daidaita tattalin arziki.
Ya daidai wannan lokacin a bara, an bayyana cewa darajar kudin Nijeriya da ke yawo a hannun mutane ya karu zuwa naira tiriliyan 3.87 a karshen watan Maris na 2024.
Wannan ya nuna karuwa daga naira tiriliyan 3.69 a watan Fabrairu da naira tiriliyan 3.65 a watan Janairu. Bugu da kari, kudin da ke wajen bankuna kuma ya karuwa a cikin kwata na farko, ya karu daga naira tiriliyan 3.28 a watan Janairu zuwa naira tiriliyan 3.41 a watan Fabrairu, kuma ya kai naira tiriliyan 3.63 a watan Maris.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp