Masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta kafa wani sabon tarihi a hutun bikin bazarar 2025, inda daga ranar 29 ga watan Janairu zuwa ranar 1 ga Fabrairu, kudaden da aka samu daga kallon fina-finai ya kai biliyan 5.75 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 802, wanda ya zarce mafi yawan kudin da aka samu a baya na yuan biliyan 5.73 a shekarar 2021.
Wannan adadi shi ne mafi yawan kudi da aka samu daga kallon fina-finai a lokacin bikin bazara a tarihin sinima ta kasar, kuma ya tabbatar da matsayin kasar Sin na kasancewa jagora wajen samun mafi yawan kudade daga kallon fina-finai wato box office a shekarar 2025, wanda ya zarce Arewacin Amurka.
- Gwamna Buni Ya Jaddada Bai Wa Sojoji Gudunmawar Kawo Karshen Boko Haram
- An Kammala Aikin Tsugunar Da Mutane A Gundumar Tingri Ta Sin Bayan Bala’in Girgizar Kasa
Bisa al’ada bikin bazara kololuwar lokaci ne na zuwa kallon fina-finai da samun riba ga masu shirya fina-finai, an samu zazzafar gasa tsakanin manyan fina-finai da aka saki. An kuma tsawaita hutun bikin bazara da kwana daya zuwa kwanaki takwas a wannan shekara, wanda ke gudana daga ranar 28 ga Janairu zuwa 4 ga Fabrairu.
Carton mai sun “Ne Zha 2” ne ke kan gaba a jerin manyan shirye-shirye, wanda ya samu sama da yuan biliyan 2.3 a cikin kwanaki hudu kacal, a cewar bayanan da kafar Beacon mai bibiyar fina-finan box office ya fitar. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)