Ya zuwa yau Litinin, kudaden da aka samu a bangaren kallon fina-finai na kasar Sin a lokacin zafi na shekarar 2025 ya zarce yuan biliyan 10, kimanin dalar Amurka biliyan 1.4, inda fina-finan da aka shirya a cikin gida suka mamaye sahun manyan fitattu uku na farko, kamar yadda dandalolin sayar da tikitin kallon fina-finai na Maoyan da Beacon suka nunar.
Kakar kallon fina-finan ta lokacin zafi a kasar Sin, wadda take farawa daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa 31 ga watan Agusta, ta kasance daya daga cikin lokutan da ake samun makudan kudaden shiga na kallo fina-finai a kasar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp