Bisa alkaluman da aka fitar a dandalin shafin intanet, ya zuwa ranar 27 ga watan, jimillar kudin shigar da kasuwar fina-finai ta Sin ta samu a lokacin zafi na bana ya zarce yuan biliyan 5, kuma adadin masu kallon fina-finai a lokacin ya kai miliyan 129.
Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yaki da hare-haren sojojin Japan da kuma yaki da mulkin danniya a duniya ko kuma yakin duniya na biyu. Daya-bayan-daya zuwa yanzu, ana ci gaba da fitar da wasu fina-finai, da shirye-shirye, da wasannim kwaikwayo, da kide-kide, da raye-raye da kuma ayyukan fasaha dake da jigon tunawa da tarihin yaki da hare-haren na Japan da kuma gadon ruhin yaki da hare-haren.
Daga cikinsu, za a fitar da manyan fina-finai guda uku dake kunshe da “Dakin daukar hoto na Nanjing” nan ba da jimawa ba. Wadannan ayyuka sun dogara ne kan hakikanin abubuwan da suka faru a tarihi, wadanda ke nuna yadda jama’ar kasar Sin suka yaki hare-haren na Japan ta bangarori daban-daban, da kuma nuna babban karfin ruhin yaki da hare-haren. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp