Kudin shigar kamfanonin kasar Sin dake cikin jerin manyan kamfanoni 500 na duniya, ya zarce na takwarorinsu na Amurka, karon farko a shekarar 2021.
Rahoton mujallar dake fitar da jerin manyan kamfanonin, ya ce kudin shigar kamfanonin Sin dake jerin, ya dauki kaso 31 cikin dari na jimilar kudin shigar kamfanonin 500, wanda ya zarce na Amurka da ya dauki kaso 30 cikin dari. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp