Bisa alkaluman da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar a kwanan nan, daga watan Janairu zuwa watan Afrilun bana, masana’antun manhajoji da ayyukan ba da hidimomin fasahohin sadarwa na Sin sun bunkasa lami lafiya, inda jimillar kudin shiga da masana’antar ta samu ta kai RMB yuan triliyan 3.8, wadda ta karu da kashi 11.6 cikin dari bisa makamancin lokaci a bara.
Abin lura shi ne, saurin karuwar jimillar ribar masana’antu ta yi yawa. Daga Janairu zuwa Afrilun bana, jimillar ribar masana’antar manhajoji ta kai RMB yuan biliyan 431.4, wadda ta karu da kashi 14.3 cikin dari bisa makamancin lokaci a bara. Kana daga Janairu zuwa Afrilu, kudin shigar da aka samu daga kayayyakin manhajoji ya kai RMB yuan biliyan 912.7, wanda ya karu da kashi 8.7 cikin dari bisa makamancin lokaci a bara, kuma ya kai kashi 24.1 cikin dari na jimillar kudaden shigar masana’antar.
A cikin masana’antar manhajoji, kudin shiga daga ayyukan ba da hidimomin fasahar sadarwa suna karuwa da sauri. Inda daga watan Janairu zuwa Afrilu, kudin shigar bangaren ya kai RMB yuan triliyan 2.4983, wanda ya karu da kashi 13.2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci a bara. Daga ciki kuma, ayyukan lissafi ta kwamfuta da manyan bayanai sun samu kudin shiga RMB yuan biliyan 410.7, wanda ya karu da kashi 14.3 cikin dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara.(Safiyah Ma)