Mamban hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar Uganda, Kugiza Kaheru, ya shaidawa wakilin CMG cewa, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta cancanci yabo, saboda ta samar da goyon baya ga kasashen Afrika a kokarinsu na raya kayayyakin more rayuwa, wanda ya biya bukatunsu na neman ci gaba.
Ta wannan hanya, a cewar Mista Kaheru, shawarar na taka muhimmiyar rawa a fannin taimakawa kasashen Afirka inganta tsare-tsaren al’umma da na tattalin arziki. Haka zalika, yadda kasashen Afirka da kasar Sin suke aiwatar da shawarar bisa tushen kare moriyar juna, ya sa ake iya gudanar da ita cikin dogon lokaci, ba tare da samun wata matsala ba.
Mista Kaheru ya fadi hakan ne a gefen taron “Demokuradiyya: Darajoji masu muhimmanci ga daukacin bil-Adama” wanda ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a kwanakin baya. (Bello Wang)