Kasar Sin ta lashe dukkan lambobin yabo na Zinare guda 10 a wasannin nutso na gasar wasannin kasashen Asiya ta Hangzhou.
Tun bayan da suka fara shiga gasar wasannin Asiya a 1974, masu nutso na kasar Sin ba su taba sakin damarsu ko da sau daya ba. Kuma yayin da ya rage kwanaki 4 a rufe gasar, yawan lambobin yabo da kasar Sin ta samu ya karuwa zuwa 316, ciki har da na zinare 171, inda Japan ke bi mata baya da zinare 37, yayin da Koriya ta Kudu ke da 33. (Fa’iza Mustapha)