Dan wasan gaban Amurka Christian Pulisic ya kammala komawa Ac Milan akan fan miliyan 20 daga Chelsea zuwa kulob din AC Milan na Italiya.
Pulisic, mai shekara 24, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru hudu da kungiyar ta Serie A, tare da zabin karin shekara daya.
Ya zira kwallaye 26 a wasanni 145 da ya bugawa Chelsea kuma ya buga wasan karshe na gasar zakarun Turai a 2021 da Manchester City.
Amma Pulisic ya zama mai dumami benci a kungiyar ta Stamford Bridge, inda ya ci sau ɗaya kawai a kakar wasansa ta ƙarshe.
A gare ni babbar dama ce ta yin fice da kuma fara sabon salo da buga kwallo a babbar kungiya irin wannan.
Chelsea ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da cinikin, inda ta ce: “Muna yi wa Christian fatan alheri tare da gode masa kan duk gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake kulob din.
Pulisic ya zo Chelsea ne daga Borussia Dortmund a kan fam miliyan 57.6 a shekarar 2019 wanda ya sa ya zama dan wasa mafi tsada daga Arewacin Amurka.
Komawarshi zuwa Seria A zai hadu da tsohon abokin wasan Chelsea Ruben Loftus-Cheek, wanda shi ma ya koma Milan a karshen kakar bana.
Chelsea ta raba gari da manyan yan wasanta a bana a kokarin ta na ganin ta rage wasu domin dauko sabon jini
Wadanda Chelsea ta raba gari dasu sun hada da Kai Havertz ya koma Arsenal, Mateo Kovacic ya koma Manchester City da kuma Mason Mount wanda ya koma Manchester United.
Cesar Azpilicueta ya koma Atletico Madrid a kyauta, yayin da sauran suka hada da Kalidou Koulibaly, Edouard Mendy da N’Golo suka koma Saudi Pro League, sun koma Al-Hilal, Al-Ahli da Al-Ittihad daya bayan daya.