Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) reshen jihar Kano, ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 15 da ta gaggauta biya musu bukatunsu ko kuma ta tsunduma yajin aikin a fadin jihar.
Yanke wa’adin a ranar Laraba ta wata wasika mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren kungiyar kuma jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Kwamared Ahmad Hazmat Sharada, ya biyo bayan wasu bukatu da ba a warware ba tsakanin ma’aikatan jinya da gwamnatin jihar tun daga watan Disambar 2023.
- Kudin Bincike Da Gwajin Kimiyya Na Sin Ya Karu Da 8.4% A Shekarar 2023
- Shugabannin Kasashen Afirka Sun Mika Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin
A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Oktoba kuma aka aika wa shugaban ma’aikatan jihar Kano, NANNM, ta yi gargadin cewa, ma’aikatan jinya da ungozoma a fadin jihar za su janye ayyukansu daga dukkan cibiyoyin kiwon lafiya da cibiyoyin horo idan gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu.
Wasu daga cikin buƙatun da aka zayyana a cikin wasiƙar sun haɗa da biyan kudaden alawus ɗin haɗari ga ma’aikatan jinya, da inganta tsarin aikin ma’aikatan jinya.
Kungiyar ta kuma bukaci a biya kashi 25 cikin 100 na tsarin biyan albashi na CONHESS, tare da wasu bukatu da aka zayyana a cikin wata tunatarwa da aka aika wa gwamnati a ranar 20 ga Agusta, 2024.
Wasikar ta kuma yi nuni da kokarin da kungiyar ta yi na tsinkayar da gwamnatin jihar ta hanyar aika wasiku, amma ba wata gamsasshiyar amsa har ya zuwa yau.
Idan har yajin aikin ya tabbata, zai iya haifar da mummunan sakamako ga tsarin kiwon lafiya na jihar saboda janye ayyukan jinya na iya haifar da dakatar da ayyuka masu mahimmanci na asibiti, lamarin da zai shafa marasa lafiya da dama a fadin jihar Kano.
Har yanzu gwamnatin jihar Kano ba ta mayar da martani kan wa’adin da NANNM ta yi ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.