Kungiyar Masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta yi fatali da sake gabatar da harajin kaso hudu na (FOB) da hukumar Kwastam ta gabatar wanda ya fara aiki tun daga ranar 4 ga watan Agustan.
Darakta janar na MAN, Mista Segun Ajayi-Kadri, ya shaida hakan a Jihar Legas, wanda ya matakin ya saba wa dakatar da cajin da gwamnati ta yi tun da farko.
- Mutane Da Dama Sun Tsere Sakamakon Harin ‘Yan Bindiga A Neja Da Kwara
- Bincike Ya Nuna Tarin Fuka Na Kashe Mutum 71,000 A Nijeriya Duk Shekara
Ya ce masana’antu suna kallon matakin zai kara janyo tsadar farashin shigo da kayayyakin sarrafa abubuwa, albarkatun kasa, injuna, da sauran kayayyakin da ba a samu a cikin gida ba.
Ajayi-Kadri ya ce kungiyar ta yi cikakken nazari kan sake gabatar da harajin na FOB wanda ta tabbatar zai kara dagula lamura ne kawai da sake jefa masana’antu cikin mawuyacin hali.
“Gaskiyar lamarin ita ce, farashin kashi hudu cikin 100 na kamfanonin ya yi yawa fiye da yadda aka samu karin kashi bakwai cikin dari da kuma karin kashi daya cikin dari na harajin tsarin shigo da kayayyaki,” in ji shi.
Ya kara da cewa, a sauran kasashen yammacin Afirka kamar Ghana, Cote d’Iboire, da Senegal, ana tsare-tsaren da aka yi niyya ko tattara kudade a tsakanin kashi 0.5 zuwa kashi daya cikin 100 na FOB, tare da karin haraji kawai kan kayan alatu ko kuma wadanda ba su da muhimmanci a shigo da su.
“Hukuncin da hukumar kwastam ta Nijeriya ta yi na bai daya na kakaba harajin kashi hudu cikin 100 na FOB zai kara tsadar kasuwanci, da karfafa hanyoyin da ba a saba gani ba, zai haifar da karkatar da kaya da kuma kara tsanani,” in ji shugaban.
Ajayi-Kadri ya nemi gwamnatin tarayya da hukumar Kwastam da su janye matakin kakaba harajin kaso hudu na FOB domin kyautata tattalin arziki ko kuma a jinkita aiwatar da hakan har sai nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp