A gobe Laraba ne kasar Sin za ta gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin kin tafarkin murdiya a matsayinta na kasa.
Game da hakan, kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin al’umma, wadda ta kunshi mutane 11,613 daga kasashe 39, kuri’ar da ta nuna gamsuwar al’ummun kasa da kasa da rawar da Sin ta taka a matsayinta na babban filin dagar gabashin duniya na fafata yakin duniya na biyu. Masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu da babbar gudummawar da Sin din ta bayar, da matukar sadaukarwarta ga burin cimma nasarar yakin.
A tsawon shekaru 14 na yakin, sojojin kasar Sin da ma fararen hular kasar, sun yi asarar rayuka miliyan 35, da tattalin arziki na sama da dala biliyan 600, kuma kasar ta yi tsayin daka, har ta kai ga murkushe aniyar mamayar dakarun kasar Japan, inda daga karshe Sin din ta zamo muhimmin fage a gabashin duniya da aka gwabza yakin duniya na biyu.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta nuna yadda kaso 73.6 bisa dari na masu bayyana mahangarsu, suka jinjinawa babbar gudummawar Sin ga cimma nasarar yakin kin tafarkin murdiya. Cikin masu bayyana ra’ayoyin daga kasashe 39, al’ummun kasashe 36 sun amince da kasancewar Sin babban fagen dagar gabashin duniya a yakin duniya na biyu, adadin da ya kai kaso 92.3 bisa dari na jimillar kasashen da aka ji ta bakinsu.
Wani abun lura a nan shi ne dukkanin al’ummun kasashe takwas na nahiyar Asiya da aka gudanar da binciken, sun yarda cewa Sin din ce babban fagen dagar gabashin duniya a yakin duniya na biyu, inda sama da kaso 70 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi daga kasashen Indiya da Malesiya suka aminta da hakan. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp