Wakilan bangarorin Falasdinawa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar Beijing a ranar Talata, kan kawo karshen rarrabuwar kawuna da karfafa hadin kan al’umman Falasdinu. Wani bincike da CGTN ya gudanar ta kafar yanar gizo ya nuna cewa, kashi 92.81 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da sahihin kokarin kasar Sin na goyon bayan hakkokin Falasdinu, da kawo karshen rarrabuwar kawuna da samar da matsaya guda tsakanin bangarorin Falasdinawa, suna masu cewa, kasar Sin ta kafa wani sabon misali na magance sabani da rashin jituwa ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.
Wannan kuri’ar jin ra’ayin da CGTN ya wallafa cikin harsunan Turanci, da Spaniyanci, da Faransanci da Larabci da Rashanci, ya samu mutane 10592 wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Mai fassara: Yahaya)