Birnin Washington D.C. na Amurka, ya zamo daya daga biranen duniya mafiya matukar hadari, kamar yadda shugaba Donald Trump ya shaida, inda ya ce, yana da shirin kwato birnin daga bata-gari. Karkashin wannan manufa, shugaban na Amurka ya kaddamar da dokar-ta-baci, don tabbatar da tsaron al’ummar birnin na Washington, kuma daya daga matakan da zai dauka a cewarsa, shi ne raba birnin da dukkanin mutanen da ba su da muhalli dake kwana a kan titunan birnin.
Game da hakan, kafar watsa labarai ta CGTN ta kasar Sin, ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar sassan kasa da kasa, wadda sakamakonta ya nuna kaso 78.7 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na ganin matakin da shugaba Trump ya ce zai aiwatar, ba zai magance matsalar tsaro dake addabar al’ummar Washington ba, kuma hakan na iya keta hurumin ‘yancin rukunin jama’a marasa muhalli, da marasa galihu da bakin haure.
Wasu alkaluma da hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ta fitar a shekarar 2024, sun nuna yadda bisa kiyasi, ake samun aukuwar muggan laifuka duk dakika 25.9 a sassan Amurka, ciki har da laifin kisan kai daya a duk mintuna 31.1, da na fyade daya a duk mintuna 4.1.
Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya kuma nuna cewa, kaso 92 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na bayyana matukar damuwa game da tsaron rayukan al’ummun Amurka, yayin da kaso 81.7 bisa dari suka ce muggan laifuka, da karuwar masu kwana a kan tituna sun zamewa manyan biranen Amurka alakakai, lamarin da ya zamo cutar Amurka mai matukar wahalar magani. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp