Yayin da ake cika shekaru 70 da kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa a bana, CGTN ta gudanar da wani bincike na kuri’ar jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,446 daga kasashe 38. Sakamakon binciken ya nuna cewa masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da nasarorin da aka samu a ci gaban tattalin arziki da zamantakewar yankin na Xinjiang. An amince sosai da cewa, tsarin gudanar da mulkin Xinjiang da kasar Sin ta yi amfani da shi ya gano hanyar da ta dace wajen daidaita ci gaba da bangaren tsaro a yankunan kan iyaka, da kara kaimi ga amfani da zamanantarwar kasar Sin a yankin Xinjiang, da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin.
A cikin binciken kuma, masu bayyana ra’ayoyi sun bayyana kalamai masu dadi game da nasarorin tattalin arziki na Xinjiang, tare da la’akari da manyan nasarori biyar da aka cimma wadanda su ne: ci gaba da inganta kiwon lafiya (da kashi 82.1), da tabbatar da damar samun ilimi ga jama’a (da kashi 81.7), da ci gaba da inganta ayyukan ababen more rayuwa (da kashi 80.8), da kuma samun babban sakamako wajen kare muhalli da gudanar da mulki (da kashi 80.6), kana da karuwar samun kudaden shiga na jama’a (da kashi 80). (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp