ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kuri’ar Kin Amincewar Amurka Ta Tsagaita Wuta A Gaza Adawa Ce Ga Bukatar Bil’adama

by CGTN Hausa
2 years ago
Amurka

Kasashen duniya sun nuna bacin rai kan kuria’ar Amurka ta kin amincewa da kudirin tsagaita wuta da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta gabatar, wanda kuma ya samu goyon bayan kasashe fiye da 100, da amincewar kasashe 13 daga cikin kasashe 15 na Kwamitin Sulhu a ranar Juma’a, inda Birtaniya ta kaurace.

Ta hanyar yin fatali da wannan kuduri, kuria’ar kin amincewar Amurka na nuni da adawarta ga bukatar Bil’adama gaba daya. Wanda ya bayyana munafurcinta a fili game da kimar da take ikirari. Ta ci gaba da ba da kariya ta diflomasiyya game da cin zarafi da ake yiwa al’ummar Gaza, Amurka tana ci gaba da sarrafa dokar kasa da kasa yadda ta ga dama, kuma a wajenta rayuwar wasu mutane ta fi ta wasu mahimmanci, shi ya sa ta daddale hannu kan a ci gaba da kisan gilla a Gaza.

  • Sin Za Ta Ci Gaba Da Sa Kaimi Ga Kare Hakkin Dan Adam
  • Shawara Ga Ma’aurata Game Da Hassada

Ga dai tambaya, ko za a samu adalci ga mutanen Gaza bayan da aka yi fatali da kiran da aka yi na tsagaita wuta? Yayin da gwamnatin Isra’ila, wacce ke da goyon bayan kasashen yammacin duniya, ta ciga da yin kisan-kiyashi a Gaza wanda ya zama abin kunya ga dukkan Bil’adama, shi ke nan Amurka ta zama kasar da ke kawo tsaiko ga samar da adalci a duniya? Ko Amurka take yi a kawar da Falasdinawa daga doron kasa? To lallai yin garambawul ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zama dole, saboda ai duniya ta fi wadannan kasashe biyar mambobin dindindin na kwamitin sulhu girma, kuma dole kudurin duniya ya yi galaba a kan bukatu da manufar wadannan kasashe biyar.

ADVERTISEMENT

Sojin Isra’ila sun kashe mutane fiye da 17,400 a Gaza, kashi 70 cikin 100 mata da yara ne tare da raunata fiye da 46,000, a cewar ma’aikatar lafiya ta Falasdinawa, wacce ta ce wasu da dama suna nan makale a karkashin baraguzan gine-gine.

Kasar Sin a kullun tana kira ga bangarorin da abin ya shafa da su mai da hankali kan manufa guda na kawo karshen rikici a Gaza, ta yadda za a baiwa al’ummar Falasdinu fatar rayuwa da zaman lafiya ta dindindin a yankin Gabas ta Tsakiya. (Muhammed Yahaya)

LABARAI MASU NASABA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
Daga Birnin Sin

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
Next Post
Ban Yi Nadamar Kashe Mahaifiyata Ba – Matashi

Ban Yi Nadamar Kashe Mahaifiyata Ba - Matashi

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.