Kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin, na ci gaba da shan suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gabatar ya nuna yadda akasarin masu bayyana mahanga suka amince da cewa, matakin na Takaichi tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma akwai bukatar gaggauta sanya ido kan karuwar burikan wasu jagororin Japan masu tsattsauran ra’ayi, na ruguza odar kasa da kasa ta bayan yakin duniya na biyu.
Kaso 91.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin kamata ya yi Japan ta gyara tarihin ta’asar da ta aikata ta hanyar aiwatar da matakai na hakika, ta kuma martaba dukkanin ikon mulkin kai da kare kimar yankunan kasar Sin. Kazalika, kaso 88.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun soki lamirin yadda Japan ta yi karan-tsaye ga odar kasa da kasa ta bayan yakin duniya na biyu.
Bugu da kari, kaso 86.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun soki kalaman Takaichi, ganin yadda suka yi matukar keta tanade-tanade na hakika, dangane da batun yankin na Taiwan, da keta hurumin takardun siyasa hudu wadanda Sin da Japan suka daddade, wanda hakan ya yi matukar illata tushen alakar Sin da Japan.
Har wa yau, kaso 88.9 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun yi Allah wadai da kalaman Japan, na yunkurin tsoma baki cikin batun Taiwan, da yi wa kasar Sin barazanar soji, suna masu cewa irin wadannan kalamai za su yi matukar barazana ga zaman lafiya da daidaito a shiyyar. (Saminu Alhassan)













