Tsarawa da aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar bisa tsari na kimiyya, muhimmin yanayi ne na nuna kwarewa, kuma babban fifiko ne a fannin jagorancin kasar Sin. Nan da dan lokaci za a fitar da shirin karo na 15, kuma tuni ya fara jan hankalin al’ummun kasa da aksa.
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, wadda masu bayyana ra’ayoyi 47,000 daga kasashe 46 suka shiga kuma ake gudanar da ita cikin shekaru uku a jere, ta shaida gamsuwar masu bayyana ra’ayoyin da kwarewar Sin ta fuskar jagoranci, da matakan aiwatarwa, da ingancinsa, sun kuma bayyana kwarin gwiwarsu ga karin bunkasar tattalin arzikin kasar.
An gudanar da kuri’un cikin shekaru uku a jere, kuma adadin masu bayyana nasarar kasar Sin ya ci gaba da wanzuwa kan sama da kaso 84 bisa dari. Cikin adadin masu bayyana ra’ayin daga kasashe masu tasowa, da masu samun saurin ci gaba, gamsuwarsu ta haura kaso 92 bisa dari. Sai kuma na masu bayyana gamsuwa ga ingancin jagorancin Sin, da kyautatuwar ababen more rayuwa, da bunkasar ilimi, da karuwar kudaden shiga, da su ma suka samu babban matsayi na gamsuwa, inda ko wannensu ya haura kaso 70 bisa dari.
Kuri’un na jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani, sun tattaro ra’ayoyin jama’a daga manyan kasashen duniya masu tasowa, da ma na kasashe masu samun saurin ci gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














