Hukumar kula da muhalli ta jihar Kwara ta rufe gine-gine 14 saboda saɓa ka’idojin muhalli, musamman saboda rashin tsaftataccen banɗaki.
Gine-ginen da aka rufe suna cikin Sabo-Oke (gine-gine 8) da titin Onikun-Kewu, Adabata (gine-gine 6), a cikin kananan hukumomin Ilorin ta Kudu da Ilorin ta Yamma.
- Mutane 4 Sun Rasu Sanadin Kwalara A Adamawa
- Kwangilar Biliyan 30: PDP Ta Bukaci EFCC Ta Binciki Gwamnatin Sakkwato
Kwamishiniyar Muhalli ta jihar, Hajiya Nafisat Musa Buge, ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Ta kuma jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaftar muhalli domin dakile cutar kwalara da sauran cututtuka dake barazana ga kiwon lafiya.
Buge ta tabbatar wa jama’a cewa, za a ci gaba da gudanar da bincike a dukkanin kananan hukumomi 16 da ke jihar domin tabbatar da bin dokokin muhalli. Ta bukaci masu gidaje da su samar da tsaftatattun bandakai a gidajensu, sannan ta yi gargadin cewa, rashin bin ka’ida zai kai ga gurfanarwa a kotu a karkashin sashe na 5, karamin sashe na 2 na dokokin muhalli na jihar Kwara.
Kwamishiniyar ta yi kira ga masu haya a yankin da su goyi bayan kokarin gwamnati na samar da tsaftataccen muhallin rayuwa ga kowa da kowa.